Hukumar alhazai ta jihar Jigawa ta ce za a fara jigilar maniyatan jihar nan zuwa kasa mai tsarki a ranar 18 ga wata.
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta ce za a fara jigilar maniyatan jihar nan zuwa kasa mai tsarki a ranar 18 ga wata.
Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya sanar da hakan a lokacin taron farko da tawagar Amirul Hajj na bana kuma mai martaba sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussain Adamu.
Ya ce za a yiwa maniyatan jihar Jigawa sawu biyu da suka hadar da jirgin farko a ranar lahadi 18 ga wata yayinda za a yi jirgi na biyu a ranar 20 ga wata.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma shedawa amirul Hajj cewar hukumar ta kammala duk wani shiri na samun nasarar aikin hajjin bana , inda ya ce tuni suka kammala aikin bizar maniyata da kuma samar musu da kudaden guzuri.
Yana mai cewar gwamnatin jiha ta baiwa hukumar duk wani hadin kai da goyan baya domin samun nasarar.
A nasa jawabin amirul Hajj kuma mai martaba sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussain Adamu ya yaba da shirye shiryen da hukumar ta yi wajen samun nasarar gabatar da aikin hajjin bana.
Ya ce bisa laakari da bayanan da shugabannin hukumar ya yiwa tawagar ta amirul Hajj sun gamsu da tsare tsaren da hukumar tayi na aikin hajjin bana.
Mai martaba sarki ya bada tabbacin tawagar na yin aiki tare da jamian hukumar domin samun nasarar aikin hajjin bana
Ya kuma yabawa gwamnatin jiha bisa basu wannan dama tare da alkawarin sauke nauyin dake kansu.