Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kaddamar da Kwamitin hana rikicin Manoma da Makiyaya domin magance rikice-rikicen da ke faruwa a tsakanin wadannan kungiyoyi guda biyu.
Bala ya kaddamarwar da kwamittin ne a ranar Asabar yayin taron Ma’aikatar harkokin kananan hukumomi da Masarautu ta jihar Bauchi.
Gwamnan ya bayyana cewa jihar, kamar sauran wasu sassan Najeriya, na fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, wanda hakan ke haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya bayyana cewa samar da wannan kwamiti ya zama dole domin a magance matsalolin da gaggawa da kuma dakile su tun kafin su kara ta’azzara.
Bala Muhammad ya bukaci mambobin kwamitin da su yi amfani da kwarewarsu da hikimarsu wajen sauke nauyin da aka dora musu.