PDP Za Ta Mutu A Disamba 2025, Ganduje ya mayarwa Lamido martani
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rahotannin shirinsa na sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a matsayin kanzon kurege.
Yayin da yake jaddada goyon bayan sa ga jam’iyyar APC, ya ce maimakon zuwa PDP nan ba da dadewa ba APC za ta karbi Sule Lamido a cikin ta.
Ganduje a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Edwin Olofu ya fitar, yana mayar da martani ne ga wani tsokaci da aka danganta ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido na cewa nan ba da jimawa ba jam’iyyar APC za ta wargaje kuma wadanda a baya suka bar PDP ciki har da Ganduje za su dawo.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayyana wannan ikirarin a matsayin mara tushe kuma wanda hankali ba zai dauka ba, yana mai jaddada cewa babu dalilin da zai sa ya fice daga jam’iyya mai mulki saboda abin da ya bayyana a matsayin gazawar ‘yan adawa.
Ganduje ya yi hasashen cewa “PDP za ta ruguje a karshen 2025”, bisa rigingimun cikin gida a jam’iyyar.