Ganduje na hutu ne da wasu uzurai a Landan tare da iyalansa bayan barin sa ofis a matsayin Shugaban Jam’iyya In ji Muhammad Garba
A cewar wata sanarwa da tsohon shugaban ma’aikata na shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Malam Muhammad Garba, tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bai samu damar halartar ziyarar shugaba Bola Ahmed Tinubu zuwa Kano ba ne sakamakon wasu ayyukan da ya riga ya tsara a Landan.
Garba ya bayyana cewa Ganduje ya yi kokari sosai don ganin ya halarci ziyarar ta’aziyyar da shugaba Tinubu ya kai gidan marigayi Alhaji Aminu Dantata, amma hakan ya ci tura saboda yana kan wasu muhimman ayyuka da ya tsara kwanaki biyar bayan murabus dinsa daga shugabancin jam’iyyar APC.
Duk da haka, sanarwar ta kara da cewa Ganduje ya tattauna da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar a jihar Kano kamar Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa, da Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC a jihar. Ya kuma basu umarnin gudanar da duk tsare-tsaren da suka dace domin tabbatar da nasarar ziyarar shugaban kasa a jihar.