‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar malamin Jami’ar Prince Abubakar Audu da ke Jihar Kogi yayin da yake lalata da wata daliba a ɗakin otel, bayan shan maganin ƙarfafa maza a karo na biyu.

0 833

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar wani malami a Jami’ar Prince Abubakar Audu, wadda ke Anyigba, bayan da aka ce ya yanke jiki ya fadi yayin da yake saduwa da wata dalibarsa a otel.

Rahotanni sun bayyana cewa malamin, wanda a bayyana sunansa ba, ya sha maganin ƙara kuzari a karo na biyu yayin da yake tare da dalibar. Sai dai hakan ya janyo masa illa, inda ya rasu kafin a kai shi asibiti.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Ovye Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an fara bincike domin gano cikakken hakikanin abin da ya faru. Ana kuma sa ran za a yi cikekken bincike na likatanci domin gano musabbabin mutuwar.

Leave a Reply