Gomnan Jahar Kaduna, Malam Uba Sani, Yace Ba Zai  Huta Ba Sai An Ceto Mutanen Kurmin Wali

0 163

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ceto mutanen da aka sace a ƙauyen Kurmin Wali na ƙaramar hukumar Kajuru.

Ya bayyana cewa yana bibiyar aikin jami’an tsaro kai tsaye, kuma ba zai gajiya ba har sai an kubutar da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su.

Rahotanni sun nuna cewa a ranar Lahadi wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Kurmin Wali inda aka ce sun sace sama da mutane 170.

Da farko hukumomi sun musanta faruwar lamarin, amma daga baya gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutane a ƙauyen.

Ya jaddada cewa gwamnatin Kaduna ba ta siyasantar da batun tsaro, yana mai cewa masu yin haka za su ji kunya.

Gwamnan ya ƙara da cewa ya gana da manyan jami’an tsaro na ƙasa domin haɗa kai cikin gaggawa wajen dawo da mutanen da aka sace.

Leave a Reply