Gwamna Namadi ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta PDP tana dab da rasa duk wata madafa a jihar Jigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta PDP tana dab da rasa duk wata madafa a jihar, inda ya ce har yanzu APC ce ke da karfi kuma zata karbe kujerun majalisun tarayya guda uku da PDP ta lashe a zaben 2023.
Gwamnan ya fadi hakan ne yayin taron “Gwamnati da Jama’a” da aka gudanar a karamar hukumar Dutse, inda ya jaddada cewa ayyukan raya kasa da shirye-shiryen gwamnatin APC na jiha da tarayya sun inganta rayuwar jama’a, wanda hakan ya kara tabbatar da amincewa da tsarin jam’iyyar ta APC.
Namadi ya ce mutanen yankin Jigawa ta Tsakiya da suka hada da mazabun Buji/Birnin Kudu da Dutse/Kiyawa sun tabbatar masa da cewa ‘yan majalisar tarayya na PDP da suka zaba ba sa wakilcin da ya kamata, kuma yanzu jama’ar sun fahimta tare da niyyar kawar da su a 2027.
Ya kara da cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya tabbatar masa da cewa aikin bututun ruwan Dutse, da layin dogo daga Maradi zuwa Dutse, da kuma hanyar Kano zuwa Maiduguri za su kammala ba tare da jimawa ba, domin tabbatar da ci gaba a Jigawa.