Wasu mazauna jihar Jigawa sun bayyana takaici da bacin rai kan yadda kamfanin rarraba wuta na Kano, KEDCO, ke cajin su makudan kudade duk da yawan dauke wutar lantarki da ake fuskanta a kwanakin nan.
Mutane da dama daga unguwanni kamar Takur, da Limawa da Godiya Miyatti a Dutse sun bayyana cewa an kara musu kudin lantarki ba tare da samun wadatacciyar wuta ba, inda wasu ke fuskantar caji har na naira 28,000 a wata daya kan wutar daki daya kacal.
Duk da ikirarin Ministan Wuta na cewa ba za a caji mutane yayin da babu wuta ba, amma KEDCO na ci gaba da watsi da wannan umarni, lamarin da ya janyo cece-kuce da kiran gwamnati da hukumomin da suka dace su sa baki.
Mai magana da yawun KEDCO, Sani Bala, ya alakanta matsalar da jahiltar tsarin cajin lantarki, inda ya ce kamfanin yana bin ka’idojin hukumar kula da wutar lantarki ta kasa, kuma suna da tsarin karbar korafe-korafe da gyaran lissafin da ba daidai ba.