Rukunin farko na alhazai 550 daga Jihar Jigawa sun tashi zuwa kasa mai tsarki don aiwatar da aikin Hajjin bana, inda jirginsu ya tashi daga filin jirgin saman Nuhu Muhammadu Sunusi da ke Dutse a daren jiya Litinin.
A wajen yi musu fatan alheri da kaddamar da jirgin farko, Gwamna Umar Namadi ya bukaci alhazan da su kasance jakadu na gari na jihar da kasa baki daya, tare da rokon su da su yi addu’o’i domin zaman lafiya da cigaban Najeriya da Jigawa yayin gudanar da ibadarsu.
Gwamnan ya kara da cewa alhazan sun kasance masu halaye nagari da ke nuna dabi’un da al’ummar Jihar Jigawa ke mutuntawa, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da kula da jin dadinsu har zuwa dawowarsu. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Ahmed Labbo, ya bayyana cewa alhazan sun fito daga kananan hukumomi 24, tare da yabawa hadin kai daga hukumomin tsaro da goyon bayan Gwamna Namadi, yayin da Daraktan Ayyuka na hukumar, Sabo Aujara, ya tabbatar da cewa an dauki duk matakan da suka dace tare da hadin gwiwar hukumomin tarayya domin wayar da kan alhazai kan kayayyakin da suka dace da kuma wadanda suka haramta, kafin jirgin Max Air 747 ya daga da su da misalin karfe 10:30 na daren jiyan.