Hukumar Hajji ta Najeriya ta gudanar da gwajin abinci dan tabbatar da ingancin abincin mahajjatan Najeriya
Hukumar Hajji ta Najeriya NAHCON ta gudanar da gwajin abinci na musamman a ofishin Rawaf Mina da ke Makkah, a wani mataki na tabbatar da ingancin abinci ga mahajjatan Najeriya.
Gwajin, wanda Jami’in hukumar a Makkah, Alidu Shutti, ya jagoranta, ya mayar da hankali ne kan dandano, da daraja, da ingancin sinadaran abincin da za a raba wa mahajjata a wuraren Mina, da Arafat da Muzdalifa.
Shugaban kamfanin Rawaf Mina, Zuhaer A. Sadayu, ya tabbatar wa da NAHCON cewa an naɗa kwararren mai kula da abinci da zai tabbatar da cewa kowane mataki na shirye-shiryen abinci ya kasance cikin tsari.
A halin yanzu, mahajjata 25,702 daga jihohi 12 na Najeriya sun isa Madina domin ziyarar masallacin Manzon Allah (SAW), yayin da NAHCON ke shirin karɓar su a Makkah don aiwatar da manyan ayyukan hajji.