Matatar Dangote za ta ci gaba da daidaita farashin fetur duk da hauhawar farashin a kasuwannin duniya

0 425

Matatar Dangote ta tabbatar da aniyar ta na ci gaba da daidaita farashin fetur duk da hauhawar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Jami’in kula da harkokin yada labarai da dabarun talla na kamfanin, Anthony Chiejina, ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna jajircewar kamfanin wajen sauƙaƙa wa ’yan Najeriya da tallafa wa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce kamfanin yana aiki da manufar gwamnati ta ‘Nigeria First’, inda ake fifita kayayyakin da aka samar a cikin ƙasa, kuma yana alfahari da gudunmawar sa wajen rage kashe kuɗin waje da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Kamfanin ya rage farashin fetur daga naira 865 zuwa 835 a watan da ya gabata, kuma ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa shirin musanyar Naira da danyen mai da ya ba wa kamfanin dama wajen rage farashin domin amfanin ’yan ƙasa.

Leave a Reply