Gwamna Umar Namadi ya bayyana shirye-shirye na gaggawa don hana ambaliya kafin kakar damina ta 2025, musamman a karamar hukumar Guri da aka fi samu ambaliya.
A wani taron da ya gudana a Dutse, gwamnan ya ce gwamnati na aiki kafada da kafada da hukumomin agaji bisa rahoton da hukumar ruwa ta ƙasa (NIHSA) ta bayar da ke nuna cewa wasu ƙananan hukumomi 20 na fuskantar haɗari.
A wajen taron masu ruwa da tsaki da hukumar NEMA ta shirya, darakta Nura Abdullahi ya ce wayar da kai da shiri a kan lokaci su ne ke rage haɗari da asarar rayuka. Gwamna Namadi ya tabbatar da cewa gwamnati ta tanadi dabaru da kayan aiki domin kare rayuka, gonaki da ababen more rayuwa kafin ambaliya ta kawo barazana.