A ƙasar Saudiyya, an rufe aikin Hajjin bana cikin nasara ba tare da wani IbTIla’i ba, inda sama da mutane miliyan 1.67 suka kammala ibadar ciki har da dubban ‘yan Najeriya.
Hukumar Hajji ta Ƙasa ta bayyana cewa jiragen sauke maniyyata za su fara sauka daga ranar 9 ga watan Yuni, wanda hakan ke nuna ƙarshen tafiyar ibada ta shekarar Hijira 1446.
Ɗan majalisar sarautar Makkah, Saud bin Mishaal, ya yaba da jagorancin Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, yana mai cewa tsari mai kyau da bin doka daga maniyyata ne ya haifar da nasarar aikin Hajjin bana.
Yayin da ake shirin fara shirye-shiryen Hajjin 2026, hukumomin Saudiyya sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da kula da wuraren ibada da tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai.