Gwamna Namadi ya jaddada cewa APC daga sama har zuwa kasa za ta ci gaba da inganta rayuwar al’umma

0 136

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada cewa gwamnatin jam’iyyar APC daga matakin tarayya har zuwa ƙananan hukumomi za ta ci gaba da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar al’umma.

Ya bayyana haka ne a lokacin taron “Gwamnati da Jama’a” da aka gudanar a Guri, inda gwamnatin jihar ke bayyana nasarorin da ta samu da kuma karɓar korafe-korafe daga jama’a.

A yayin taron, gwamnan ya karɓi kundin buƙatun al’ummar yankin, inda ya tabbatar da cewa za su duba su domin aiwatar da duk abin da ya dace.

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, ciki har da Sanata Ahmad Abdulhamid Malam Madori da Hon. Abubakar Fulata, inda jama’ar Guri suka nuna gamsuwarsu da ayyukan gwamnati.

Leave a Reply