Jam’iyyar APC reshen Jigawa ta amincewa da Gwamna Namadi a matsayin ɗan takararta tilo a zaɓen 2027

0 645

Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Umar Namadi tare da amincewa da shi a matsayin ɗan takararta tilo a zaɓen 2027.

Wannan matsaya ta fito ne a yayin taron “Gwamnati da Jama’a” da aka gudanar a ƙaramar hukumar Guri, inda tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Hon. Faruk Adamu Aliyu, ya buƙaci jam’iyyar ta tsaya tsayin daka wajen mara wa gwamnan baya.

Dukkan wakilan majalisa da suka halarci taron sun amince da ƙudirin, bisa la’akari da gamsuwa da yadda Gwamna Namadi ke tafiyar da mulki da ci gaban jihar.

Wannan matakin na jam’iyyar APC ya fito a daidai lokacin da fagen siyasar zaɓen 2027 ke fara ɗaukar zafi, inda ake ganin hakan zai ƙarfafa jam’iyyar wajen ci gaba da shimfiɗa tsare-tsaren ci gaba.

Leave a Reply