Gwamnan jihar Kogi ya jajantawa iyalan wadanda hatsarin mota ya rutsa da su a kasuwar Obajana

0 113

Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Ododo ya jajantawa iyalan wadanda hatsarin mota ya rutsa da su a kasuwar Obajana a daren Lahadin da ta gabata wanda yayi sanadiyar salwatar rayukan mutane goma sha uku da raunata mutune biyu.

Gwamna Ododo wanda ya samu rahoton faruwar hatsarin a jiya Litinin, ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa, ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin jihar tana tare dasu a lokacin da suke cikin bakin ciki.

A cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ismaila Isah ya fitar, ya ce gwamnan ya damu matuka da hatsarin na yammacin ranar Lahadin, lamarin da ya haifar da rasa rayuka da kuma haddasa gobara a inda lamarin ya faru. Gwamna Ododo ya yabawa jami’an bayar da agajin gaggawa a jihar kan yadda suka tashi tsaye wajen ganin sun shawo kan gobarar da ta tashi biyo bayan hadarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: