Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, ya ce yankin Arewa ta Tsakiya ya fi yankin yankin Igbo cancantar ya yi takarar shugaban kasa a 2023

0 77

Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, ya ce yankin Arewa ta Tsakiya ya fi yankin yankin Igbo cancantar ya yi takarar shugaban Kasa a shekarar 2023.

Gwamna Bello, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan, ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari.

A cewarsa, yankin Arewa ta tsakiya shine yankin da ya kamata a bawa damar yin shugaban kasa, biyo bayan yadda aka mayar yankin koma baya tun shekarar 1960 bayan Najeriya ta samu yancin kai.

Yahaya Bello, ya ce ya kawowa shugaba Buhari ziyara ne domin fadakar da shi kan yanayin tsaro da Jihar Kogi ta ke ciki, inda ya kara da cewa yankin Arewa ta Tsakiya basu taba samun Shugaban Kasa ko kuma Mataimakin Shugaban Kasa ba.

Haka kuma ya ce domin adalci ya zauna, akwai bukatar a bawa yankin damar fitar da shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Ga fannin tsaro kuma da Jihar take ciki, Gwamna Yahaya Bello, ya ce mai yuwuwa hakan yana da alaka da siyasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: