Gwamnatin Jihar Jigawa na kashe kudi naira miliyan dubu biyar a kowace shekara wajen samar da magunguna ga asibitocin Jihar

0 182

Gwamnatin Jihar Jigawa na kashe kudi naira miliyan dubu biyar a kowace shekara wajen samar da magunguna ga asibitocin Jihar nan.

Kwamishinan harkokin kiwon lafiya na Jiha, Dr. Muhammad Abdullahi Kainuwa ya bayyana haka lokacin da yake kaddamar da kwamatin tabbatar da dorewar shirin samar da magunguna ga asibitoci mai wakilai goma sha takwas a ofishin sa.

Kwamishinan ya kara da cewa ana kashe fiye da naira miliyan dubu daya daga cikin adadin wajen kula da lafiyar masu karamin karfi kyauta da suka hadar da Mata masu juna biyu da kananan yara yan kasa da shekara biyar da dai sauransu.

Dr. Muhammad Abdullahi Kainuwa ya kuma jaddada kudirin Gwamnatin Jiha wajen samar da magunguna masu ingancin da rahusa ga al’ummar Jihar nan, inda ya bada umarnin saye da samar da magunguna daga kamfanin samar da magunguna na Jihar Jigawa.

Daga nan sai kwamishinan ya bukaci wakilan kwamatin dasu rika sa ido tare da daukan matakai wajen aiwatar da shirin a asibitoci domin tabbatar da gaskiya da sadaukar da kai a tsakanin ma’aikatan lafiya wajen gudanar da aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: