Gwamnatin jihar kaduna ta amince da kashe naira miliyan 81 ga masu bincike 13, domin yin nazarin bangarori daban daban na sake fasalin ilimi a jihar, tin bayan zuwan gwamnatin Nasir El-Rufa’i.

Cikin wata sanarwa da mai baiwa Gwamnan jihar shawara kan kafofin yada labarai da sadarwa Mr Muyiwa Adekeye ya fitar, ya bayyana cewa kwamitin zartarwa na jihar ya amince da shirin wanda Gwamna Nasir El-Rufa’i ke jagoranta.

Adekeye yace, kwamishinan ilimi Dr Shehu Usman Muhammad yayi bayanin cewa an zabi mutane 13 ne daga cikin mutane 75 da aka gabatar.

Tunda farko ma’aikatar ta fitar da goron gayyata ga kwararrun masu bincike a fannin a watan octoban shekarar data gabata, yayinda aka samu masu bincike 75 da suka nuna sha’awarsu, kamar yadda sanarwar ta Ambato kwamishinan na bayyana haka.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: