Gwamnatin Taraba Ta Sanya Dokar Takaita Zirga-zirga A Jalingo

0 92

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya saka dokar hana zirga-zirga a garin Jalingo biyo bayan sabbin hare-hare da aka kai kan al’ummar Kona da ATC da ke kusa da Jalingo.Gwamnan ya fitar da wannan sanarwa ta hannun babban mataimakinsa na musamman akan yada labarai mista Bala Dan Abu.

Gwamnan ya ce za a takaita zirga zirgan al’umma daga karfe hudu na yamma zuwa karfe shidda na safe biyo bayan hare-haren da aka kai, kuma wannan doka ta shafi wuraren da aka kai harin da garin Jalingo.Ya kara da cewa an tura jami’an tsaro wuraren domin tabbatar da cewa mutane sun bi doka, tare da gaggauta samar da zaman lafiya a cikin al’umma.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya ce an samu gudun hijira na mata da yara da dama daga wureren da rigimar ya faru zuwa garin Jalingo biyo bayan harbe-harbe kan mai uwa da wabi, da kone-konen gidaje.

A ranar lahadin da ta gabata 16, ga watan Yuni shekarar 2019, rigima ta barke irin wanda ya taba faruwa a watan Afrilun shekarar nan amma sai jami’an tsaro suka kwantar da tarzomar. Sai dai a jiya litinin rigimar ta kuma ballewa, kuma hakan ne ya yi sanadin sanya dokar hana zirga-zirga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: