Gwamnatin tarayya zata dukufa wajen inganta ilimin yara mata a Najeriya

0 293

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya sanar da wata tawaga daga Amurka cewar gwamtanin tarayya ta dukufa wajen magance matsalolin ilimin yara mata da kuma karfafar su, tare da samar da manufofi da shirye-shirye da zasu bunkasa fannin mata.

Mataikamakin shugaban kasar ya karbi bakuncin tawagar ne wanda mataimakin babbar sakatariyar amurca kuma shugaban magamayyar kungiyar bunkasa cigaba nai dorewa Amina Mohammad ta jagoranta zuwa fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yayin ziyarar samu rakiyar babban jami’in Asusun Malala, Malala Yousafari da sauran jami’ai.

Shattima ya tabbatar da himmatuwar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dangane da lamuran ilimin mata da karfafar mata, lura yadda ya jajirce waen bunkasa ilimin mata da kirkirar damarmaki.

Daga nan mataimakin shugaban kasar ya bayar da tabbacin gwamnatin tarayya zata yi gamayya da kungiyar domin cigaban kasa.

A nasa jawabin mataimakin babbar sakatariyar Amurkan Amina Mohammad ya yabawa gwamnatin tarayya da yunkurin ta na Muradin cigaba mai dorewa wajen daidaito a fannin damar makin ilimi tsakanin yara mata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: