Gwamnnan Jihar Borno Baba Gana Zulum Ya Ce Bai San Wanda Zai Gaje Shi Ba A 2027

0 135

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa bai san wanda zai gaje shi ba bayan karewar wa’adin mulkinsa a watan Mayun 2027.

Da yake magana a ƙarshen mako a wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar a Maiduguri, Zulum ya jaddada cewa gwamnatinsa ta fi maida hankali ne kan ƙarfafa tsaro da kuma samar da muhimman ayyukan ci gaba ga al’ummar jihar.

Ya ce yana da ƙudurin tabbatar da adalci, gaskiya da kuma tsari na dimokaraɗiyya wajen zaɓen shugabannin jam’iyya a manyan takarkarun jam’iyyar da ke tafe.

A cewarsa, ingancin tsari da gaskiyar zaɓen suna da matuƙar muhimmanci domin haɗin kan jam’iyyar da nasarar ta a nan gaba, yana mai kira da a samar da sababbin mutane da za su rike muƙamai daban-daban na jam’iyyar.

Gwamnan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su bar sababbin fuskoki su fito ta hanyar tsarin dimokaraɗiyya, domin ƙarfafa tushen jam’iyyar a ƙasa da kuma tabbatar da haɗin kai da wakilci ga kowa.

Yayin da yake watsi da jita-jitar cewa yana da tasiri kan tikitin jam’iyyar a nan gaba, Zulum ya tabbatar a fili cewa bai naɗa ko goyi bayan wani ɗan takara ba, ko don muƙaman jam’iyya ko kuma wani muƙamin zaɓe.

Ya ce: “Ba ni da ɗan takara ga kowani matsayi, kuma ban san wanda zai gaje ni ba. Na miƙa zaɓin shugabanni ga Allah Maɗaukaki, bisa ga tsarin dimokaraɗiyya da ra’ayin mambobin jam’iyya da al’ummar Jihar Borno.”

Leave a Reply