HARIN TUDUN BIRI: Sanata Abdul’aziz Yar’Adua ya bayyana harin a matsayin babban kuskure

0 170

Shugaban kwamitin sojoji na Majalisar Dattawa Sanata Abdul’aziz Yar’Adua, ya bayyana harin jirgi maras matuki da yayi sanadiyyar kashe mutane da dama a Kauyen Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna a matsayin babban kuskure.

Sanata Yar’Adua ya yaba da yadda shugaban rundunar tsaron kasar nan ya Amshi laifin wannan kuskure.

Abdul’aziz Yar’Adua, yayi tsokaci dangane da kiraye-kirayen kungiyar Dattawan arewa na cewa manyan sojojin kasar nan suyi Ritaya, sakamakon wannan hari da ya kashe mutane sama da 85 a Kauyen Tudun Biri dake karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna. Kazalika, sanatan ya shawarci gwamnatin Jihar Kaduna ta umarci al’umomin Musulmi da su kauracewa haduwar mutane masu yawa a wuri guda,domin hakan zai Inganta zaman lafiya da magance matsalar tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: