Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta fara binciken wani jami’inta da ya alakanta kansa da LGBTQ

0 75

Hukumar ta kaddamar da bincike kan lamarin ne bayan bidiyon jami’in ya karade ya karaɗe kafofin sada zumunta, tare da haifar da ce-ce-ku-ce.

Shugaban Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jaddada matsayin hukumar na yaki da ’yan luwadi da madigo da dangoginsu, ya na mai nuni da dokar Shari’ar Musulunci ta jihar da ta haramta auren jinsi.

A wani bidiyo da ya yadu, an ga wani wani mutum da ke ikirarin cewa shi jami’in Hisbah ne taron kungiyar LGBTQ, inda yake kira da a ba su dama tare da kare hakkokin mambobinsu.

Da yake tabbatar da cewa wanda ke cikin bidiyon ma’aikacin Hisbah, Sheikh Daurawa ya bayyana, amma ya halarci taron kungiyar ne a kashin kansa, ba da yawun hukumar ba, kamar yadda ya yi ikirari.

Shaikh Daurawa ya ce hasali ma, Hisbah yaki take yi da kungiyoyin masu nema da auren jinsi da kuma ’yan daudu a jihar. Daurawan ya kara da cewa Hisbah ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tunkarar duk wata kungiya ko wani mutum da ke tallata ’yan LGBTQ a jihar, inda ya shawarce su da su bar Kano saboda ba su da wurin buya a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: