Hukumar ‘yan sanda na ci gaba da yaki da laifuffukan yanar gizo a kasar nan

0 115

A ranar Talata, Sufeto-Janar na ‘yan sandan, Kayode Egbetokun, ya ba da umarnin fadada ayyukan rundunar ‘yan sandan, a cibiyar yaki da laifuffukan yanar gizo (NPF-NCCC), zuwa ofisoshin da ake da su na sashen binciken manyan laifuka domin saukaka gudanar da ayyukan da ya dace, na dokar da aka gyaran 2024.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce, a yanzu hukumar za ta samu ofisoshin aiki a ofisoshin da ke jihohin Legas, Kaduna, Gombe, da kuma Enugu.

Yace hakan  zai taimaka wajen daidaitawa tare da sa ido wajan gudanar da bincike cikin sauki na laifukan da suka shafi yanar gizo da aka kai rahoto ga ‘yan sanda. Shugaban ‘yan sandan ya ce fadada Cibiyar za ta kara habaka karfin yakar laifukan yanar gizo, da ba da damar daukar matakan gaggawa da hadin gwiwa kan barazanar intanet a fadin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: