INEC ta ce za ta sake gudanar da zaben cike gurbi a fadin kasar nan a watan Fabrairun 2024

0 199

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ce za ta sake gudanar da zaben cike gurbi a fadin kasar nan a watan Fabrairun 2024, domin gibin wuraren da ake da su a majalisun dokokin jihohi da na tarayya.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shine ya bayyana haka a wani taro da ya yi da shugabannin  jam’iyyun siyasa jiya a Abuja.

Yakubu ya kara da cewa, kotunan sauraren kararrakin zabe sun umurci hukumar da ta sake gudanar da zabe a mazabu 34 na tarayya da na jihohi, wanda ya kunshi na majalisar dattawa, mazabar tarayya 11, da kuma mazabu 22 na jihohi. Ya bayyana cewa za a sake gudanar da zaben ne tare da zaben fidda gwani, inda ya kara da cewa dole ne jam’iyyun siyasa su gudanar da sabon zaben fidda gwani a cikin takaitaccen lokaci kamar yadda doka ta tanadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: