IPAC ta amince da dage zaben kananan hukumomin jihar Yobe da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba, 2023

0 290

Kungiyyar hadin kan jami’iyyun siyasa (IPAC) reshen jihar Yobe, ta amince da matakin da aka dauka na dage zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba, 2023.

Shugaban kungiyar IPAC a ranar Talata ya bukaci da a dage zaben kananan hukumomin da za a yi ranar 25 ga watan Nuwamba har zuwa lokacin damina da kuma girbin amfanin gona.

Shugaban kungiyar IPAC, wanda kuma shine sakataren majalisar Abdullahi Bello, a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, ya ce ko da yake ba su ji dadi akann yadda shugaban bai tuntube su ba yayin da suke yanke shawarar dage zaben, amma sun amince a sauya zaben.

Bello ya ce abin takaici ne yadda duk da yawancin su shugabannin hukumar IPAC ne, shugaban ya yanke shawarar ci ba tare da ya Tuntube su. Bello ya nemi afuwar magoya bayan kungiyarsu akan su kara hakuri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: