Isra’ila ta kashe wasu kananan yaran Falasɗinawa 24 a sabon harin da ta kai Rafah

0 147

Adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a hare-haren da jiragen samanta suka kai a wasu gidaje biyu a Rafah da ke kudancin Gaza ya ƙaru zuwa mutum 24, da suka haɗa da ƙananan yara 16 da mata shida, kamar yadda majiyoyi daga asibiti suka shaida wa Anadolu Agency.

Majiyoyin sun ce da dama daga cikin Falasɗinawan sun mutu ne sakamakon munanan raunuka da suka samu lokacin da jiragen yaƙin Isra’ila suka kai musu hari ranar Asabar a gabashi da tsakiyar Rafah.

Sun ce har yanzu akwai sauran mutane da ɓaraguzan gine-gine suka danne.

Ranar Asabar da maraice, rundunar ƴan sa-kai ta Gaza ta sanar da gano da dama daga cikin mutanen da aka kai wa hari a cikin gidajensu da ke gabashin Rafah.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce ma’aikanta sun gano mutanen da “jirgin dakarun mamaya ya kai wa hari a wani gini mai hawa da yawa na iyalan Abdul-Aal da ke kan Titin George a gabashin Rafah.”

Kazalika ma’aikatan sa-kai “suna ci gaba da ƙoƙarin gano sauran mutanen da suka ɓata.”

Lamarin ya faru ne a yayin da dakarun Isra’ila suke barazanar kutsawa cikin Rafah duk da gargaɗin da ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya suke yi, ganin cewa birnin shi ne wuri mafi girma da ƴan gudun hijira daga Gaza suke samun mafaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: