Jami’an hukumar Kwastam sun kama wani kwantaina maƙare da bindigogi da aka yi fasaƙwaurinsu daga ƙasar waje

0 209

Jami’an Hukumar Kwastam sun kama wani kwantaina makare da bindigogi da aka yi fasakwaurinsu daga kasar waje.

An kama kwantainar wacce ke dauke bindigogin ne a Tashar Jirgin Ruwa ta Tin Can Island da ke Jihar Legas, bayan mai kayan ya yi wa jami’an hukumar karya cewa talabijin din bango ne ya shigo da su Najeriya a cikin kwantainar.

Kakakin Hukumar Kwastam Reshen Tin Can, Uche Ejesieme, ya ce, Jami’an hukumarmu sun yi nasarar kama kwantainar, tuni kuma aka killace ta, ya zuwa lokacin kammala bincike, domin tabbatar da iya adadin makaman da kuma sauran muhimman bayanai.

Uche ya bayyana cewa, tun da farko sai da jami’an hukumar suka diga ayar tambaya a kan kayan, lura da yadda masu kula da kayan ke ta karba-karba wajen yin fitonsu.

Ya ce bayan an kammala bincike za su sanar da cikakken bayani game da miyagun makaman da aka kama ta hannun hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Hukumar ta kuma yi alkawarin yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin an kamo duk mutanen da suke da hannu a shigo da makaman, da nufin magance matsalar fasakwaurin makamai zuwa Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: