Jam’iyyar APC ta musanta batun kulla yarjejeniya da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ko NNPP

0 173

Jam’iyyar APC ta musanta batun kulla yarjejeniya da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ko NNPP kan hukuncin da kotun koli za ta yanke kan zaben gwamnan jihar.

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan a wata sanarwa jiya.

Kotun sauraren kararrakin zabe da ta daukaka kara dai sun tsige Gwamna Abba tare da ayyana dan takarar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris sai dai Abba Kabir ya daukaka kara zuwa kotun koli.

A wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya fitar, ya ce babu kamshin gaskiya a maganar sulhu tsakanin NNPP da APC domin sauya hukuncin kotun koli.

Haka kuma ya bayar da tabbacin jam’iyyar su zata samar da zaman lafiya da kyakkyawar alaka da duk kabiu da dama al’ummar jihar. Daga karshe yayi kira ga magoya bayan jam’iyyarsu ta APC da la’ummar Nigeria da su yi watsi da jita-jitar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: