Jam’iyyun Adawa Sun Kaurace Wa Zaɓen Kananan Hukumomin Bauchi

0 65

Jam’iyyun adawa sun ƙaurace wa zaɓen ƙananan hukumomin Bauchi

A yayin da ake zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Bauchi a yau Litinin, jam’iyyun adawa biyar da suka hada ƙawance sun kaurace wa zaben bisa zargin an shirya shi ne domin karya su da kuma ba wa jam’iyyar gwamnatin jihar nasara ko ta halin ƙaƙa.

Jam’iyyun da suka haɗa ƙawance sun hada da ADC, PRP, AAC, DDP da NNPP, sun yi zargin tsawwala kuɗaɗen gudanarwar zaɓen da aka ƙaƙaba wa ’yan takara da kuma saba wa dokar zaɓe ta ƙasa.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da aka gudanar ranar Lahadi a Bauchi, kakakin ƙawance, Dakta Ladan Salihu, ya zargi Hukumar Zaɓe ta Jihar Bauchi (BASIEC) da gudanar da zaɓen bisa dokar zabe ta jihar ta shekarar 2008.

Salihu ya bayyana cewa dokar ta saɓa da tanade-tanaden Dokar Zabe ta Kasa ta 2026, wadda BASIEC, lamarin da ya ce ya sanya zaɓen cikin yanayi mai rauni a bangaren doka.

Ƙawance ya kuma yi tir da abin da ya kira tsadar kuɗaɗen takara da na gudanar da harkokin zaɓe da aka ɗora wa ’yan takara, alhali gwamnati ce ke ɗaukar nauyin tsarin zaɓen baki ɗaya.

A cewarsu, kuɗaɗen sun yi yawa kuma suna iya tsiyata jam’iyyun adawa, musamman ganin yadda suke dogaro da gudummawar ’ya’yansu, yayin da jam’iyya mai mulki ke da damar amfani da dukiyar gwamnati.

Jam’iyyun sun kuma soki jadawalin zaɓen da BASIEC ta fitar, inda suka ce an fitar da cikakkun ƙa’idojin zaben ne bayan an riga an wallafa jadawalin zaɓen, wanda suka ce an yi ne ya yadda ko ta halin ƙaƙa, jam’iyya mai mulki ce za ta lashe zaɓen.

Sun yi zargin cewa kwana biyu kacal aka bai wa jam’iyyun, daga 15 zuwa 17 ga Yuli, domin gudanar da zaɓen fid-da-gwani.

Haka kuma, kwana biyu kacal aka bai wa ’yan takara, daga 22 zuwa 24 ga Yuli, domin karɓar fom din takara, da kuma wasu kwanaki biyu, daga 27 zuwa 29 ga Yuli, domin mayar da fom ɗin.

A cewar ƙawancen, wannan lokaci bai isa ba wajen shirya takardu, tantance ’yan takara, gabatar da ƙorafe-ƙorafe da kuma warware taƙaddamar zaɓe.

Sun kuma ce umarnin BASIEC na cewa a mayar dukkan fom ɗin takara a hedikwatar hukumar da ke birnin Bauchi domin tantancewa ya ƙara wa ’yan takarar yankunan karkara wahalar sufuri da sauran kuɗaɗen gudanarwa.

Kawancen ya ce, “Mun yanke shawarar kada mu kashe ko da mafi ƙarancin kuɗaɗen da ’ya’yan jam’iyyunmu suka tara da wahala a wani tsari da aka lalata sahihiyar gasa ta dimokuradiyya.”

Sun zargi hukumomin da shirya komai tun farko domin tabbatar da samun gagarumar nasara ga jam’iyyar da ke mulki.

Jam’iyyun sun jaddada cewa kauracewarsu ba alamar rauni ba ce, illa dai matakin ƙin amincewa da abin da suka kira maguɗin siyasa. Sun ce za su karkatar da kuɗaɗen da za a kashe a zaɓen wajen ƙarfafa tsarin jam’iyyunsu da wayar da kan mambobi.

Sun buƙaci a ɗage zaben kananan hukumomin nan take, har sai BASIEC ta magance ƙorafe-ƙorafen da suka gabatar tare da samar da daidaiton dama ga dukkan jam’iyyun.

Sun kuma yi barazanar ɗaukar matakan shari’a ko na siyasa da doka ta amince da su idan hukumar ta gaza magance matsalolin.

Sai dai da aka tuntubi shugabar BASIEC, Hajiya Jummai Sadiq, ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa hukumar ba ta karya wata doka ba kuma tana gudanar da zaɓen ne bisa dokokin da aka tanada.

Ta ƙara da cewa ƙauracewar ƙawancen jam’iyyun ba zai hana hukumar gudanar da zaben kamar yadda aka tsara ba.

Leave a Reply