Jigawa: Sabon Kwamishina ’Yan Sanda Ya Fara da Tsarin Tsaro Na Musamman, Ya Sha Alwashin Fatattakar Masu Laifi
JIGAWA: SABON KWAMISHINAN ’YAN SANDA YA FARA DA TSARIN TSARO NA MUSAMMAN, YA SHA ALWASHIN FATATTAR MASU LAIFI.
Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar
Jigawa, CP Tijjani Murtala, ya bayyana cewa jagorancinsa zai mayar da hankali kan ƙarfafa tsaro, yaƙi da miyagun ƙwayoyi, daba, rikicin siyasa, laifukan intanet da kuma inganta haɗin gwiwa da al’umma.
A jawabinsa na farko ga manema labarai a Dutse, ya ce rundunar za ta:
Ƙara sintiri musamman da daddare.
Tsaurara doka kan motocin da ke ɓoye lambobin rajista ba bisa ka’ida ba.
Ƙaddamar da yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye.
Dakile daba da tashin hankali na siyasa.
Ƙarfafa yaƙi da damfarar intanet da ayyukan ƙungiyoyin asiri.
Inganta tsaro a unguwanni da haɗin gwiwa da sarakuna, malamai da shugabannin al’umma.
Ladabtar da jami’an da aka samu da cin hanci, rashawa ko take haƙƙin jama’a.
CP Tijjani Murtala ya jaddada cewa Jigawa ba za ta zama mafakar masu aikata laifi ba, tare da kira ga al’umma da su riƙa baiwa jami’an tsaro sahihan bayanai domin kare rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta yi aiki cikin ƙwarewa, gaskiya, mutunta haƙƙin ɗan adam, da bin doka.