Jihohi 27 sun yi watsi da gayyatar kwamitin bincike kan kudaden N177.8Bn da aka ware musu na muhalli

0 266

Kimanin Jihohi 27 ne suka yi watsi da gayyatar kwamitin da Hukumar Yaki da korafe-korafen Jama’a ta kafa domin bincike kan kudaden da aka ware musu na muhalli a cikin watanni 33 da suka gabata wanda ya kai Naira biliyan 177 da milyan dari 8.

Jihohin su ne: Kano, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nassarawa, Niger, Osun, Oyo, Plateau, Sokoto, Zamfara, Benue, Borno da Cross-River.

Sauran sun hada da: Abia, Adamawa, Akwa-Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Delta, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe da kuma Imo.

Kwamitin yana karkashin jagorancin kwamishinan tarayya mai wakiltar jihar Ekiti, Olukayode Bamisile.

Mambobin kwamittin sun hada da kwamishinan tarayya mai wakiltar jihar Oyo, Folawiyo Bello, da takwaransa na jihar Kaduna, Abdullahi Garba Abbas.

A baya dai an yi taro da wakilan gwamnonin daga ranar 31 ga watan Yuli zuwa 16 ga watan Agusta amma yawancin jihohin sun ki halattar zaman taron.

Binciken ya shafi watan Janairu 2020 zuwa Satumba 2022 watanni 33 kenan kuma an raba kudi Naira biliyan 177 da dari 8 ga jihohi da kananan hukumomi.

Jihohin sun samu Naira biliyan 96 da milyan dari 8 yayin da kananan hukumomi kuma suka samu kudi Naira biliyan 81.

A matsakaici, wata jihar tana samun kudi Naira miliyan 65 duk wata yayin da wasu ke samun Naira miliyan 120.

Ga kananan hukumomin kowace Jiha kuwa wasu na samun Naira Miliyan 54 a duk wata yayin da wasu Naira Miliyan 98 a duk wata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: