Karancin ruwan sha ya kara ta’azzara cikin wannan shekarar a garin Fika na jihar Yobe

0 185

Karancin ruwan sha da aka dade ana fama da shi a garin Fika a jihar Yobe ya kara ta’azzara a wannan shekarar yayin da mazauna yankin ke cigaba da nuna fargaba.

Malam Ibrahim Musa Fika, wani mazaunin garin ya shaidawa City & Crime cewa garin na fama da matsalar karancin ruwa da aka shafe shekaru goma ana fama da shi wanda hakan ya sanya suka fara dogara da amfani da gurbatacciyar hanyar ruwan sha da sauran ayyukan cikin gida.

Wannan a cewarsa, ya jawo wa mazauna yankin shiga cikin wahalhalu tare da kamuwa da wasu cututtuka masu alaka da ruwa.

rahotanni sun bayyana cewa aikin samar da ruwan sha na gwamnatin tarayya anyi watsi da shi watanni kadan bayan an fara aikin. Da aka tuntubi Sanata mai wakiltar Yobe ta Kudu kuma mai gudanar da aikin, Ibrahim Mohammed Bomai, ya ce sun yi nasarar samun aikin daga gwamnatin tarayya amma kudaden bai isa a kammala shi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: