Kasuwar ƴan kwallo: Makomar Araujo, Luis Diaz, Jack Grealish da sauran wasu manyan yan wasa

0 70

Barcelona ta nuna sha’awar sayen ɗan wasan gaban Liverpool da Colombia mai shekara 27, Luis Diaz. Haka zalika, za ta yi nazari a kan tayin ɗan wasan bayan ta, kuma ɗan Uruguay mai shekara 25, Ronald Araujo a bana, kuma Manchester United tana cikin masu bibiyar ɗan wasan.

Manchester City za ta saurarin tayin ɗan wasan tsakiyar ta, kuma ɗan Ingila mai shekara 28, Jack Grealish a bana.

Arsenal da Liverpool da kuma Manchester United sun shiga takarar sayen ɗan wasan bayan Real Madrid da Faransa, ɗan shekara 28, Ferland Mendy.

Wasu ƙungiyoyin gasar Firimiya na bibiyar ɗan wasan gaban Atletico Madrid mai shekara 19, kuma ɗan Sifaniya, Samu Omorodion, wanda ke zaman aro a Alaves.

Manchester United da Newcastle na bibiyar ɗan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 29, Adrien Rabiot idan bai sabinta kwangilar sa da Juventus ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: