Kungiyar Dattawan Arewa ta bayyana damuwa da rashin jin dadi kan karin kudin wutar lantarki

0 142

Kungiyar Dattawan Arewa  a jiya ta bayyana damuwa da rashin jin dadi kan matakin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dauka na karin kudin wutar lantarki a kwanakin baya.

Ta bayyana matakin a matsayin wani mataki na sakaci da kuma rashin mutunta walwala da jin dadin al’ummar Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na kungiyar Abdul-Azeez Suleiman ya fitar, kungiyar ta datatwan arewa ta ce ta fahimci cewa wannan karin kudin wutar lantarkin zai yi mummunan tasiri ga al’ummar da ke fama da matsalar tsadar rayuwa, wanda hakan zai kara wahalhalun yan kasa. Ta ce karin zai kara zama wata barazana ga talakawan Najeriya musamman wajen biya kudin wutar lantarki a kullum.

Leave a Reply

%d bloggers like this: