Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP a Najeriya ya bayyana goyon bayansa ga Umar Damagum

0 207

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP a Najeriya ya bayyana goyon bayansa ga shugaban jam’iyyar na ƙasa na riƙon ƙwarya, Umar Damagum.

Sakataren harkokin watsa labarai najam’iyyar, Debo Ologunada, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Ya ce kwamitin gudanarwar ya nuna goyon bayan ne ga shugaban na riƙon ƙwarya a taronsa na 54 da ya gudanar ranar Talata.

Ologunagba ya ce kwamaitin ya nuna goyon bayan ne bisa la’akari da irin ƙoƙarinsa wajen sake wa jam’iyyar ta PDP fasali domin ta amsa sunanta na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya. A ranar Alhamis ɗin nan ne dai jam’iyyar za ta gudanar da babban taronta inda a nan ne za a tabbatar da ci gaba da shugabancin Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar ko kuma a tsige shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: