EFCC sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da ke Abuja

0 223

Jami’an Hukumar Yaki da masu karya tattalin arziki (EFCC) sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Kogi Bello da ke Abuja.

Wani babban jami’in EFCC da ya bukaci wakilin namu ya sakaya sunansa ya tabbatar cewa sun kai samamen ne da nufin kama da Yahaya Bello.

Sai da kuma jami’in ya ki amsa tambayar wakilin namu game da zargin da hukumar ke wa tsohon gwamnan. Ana dai tunanin samamen na da alaƙa da badaƙalar Naira biliyan 84 na jihar Kogi a zamanin mulkin Yahaya Bello da EFCC ke bincike a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: