Majalisar Ɗinkin Duniya za ta ƙaddamar da asusun neman taimako na kusan dala biliyan uku, domin samar da kayan agaji ga Falasɗinawa a Gaza da yankin Gaɓar Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.
Shugaban hukumar jin-ƙai ta majalisar wadda ke kula da yankunan Falasɗinawa, ya ce, za a yi amfani da kashi 90 cikin ɗari na kuɗin a Gaza, yayin da ma’aikatan agaji ke ta faman maganin faɗawar yankin cikin yanayi na yunwa, musamman ma a yankin arewaci.
Ya ce yayin da ake shigar da ƙarin manyan motoci maƙare da kayan abinci zuwa yankin, ya zama wajibi a sake gyara cibiyoyin samar da ruwa da na kula da lafiya da aka lalata sakamakon yaƙi da Isra’ila.
Tun a farko dai, ofishin kula da haƙƙoƙin bil adama na Majalissar Dinkin Duniya ya ce Isra’ila ta ci gaba da ƙaƙaba abin da ta kira takunkumai ba bisa ƙa’ida ba kan rarraba kayan jin ƙai a Gaza – wani abu da gwamnatin Isra’ila ke musantawa.