Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da ƙudirin dokar kare yara daga cin zarafi

0 198

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da kudirin dokar kare yara daga cin zarafi.

Sai dai kudirin dokar ya cire sashen da ya kayyade shekarun aurar da ‘yanmata saboda addini.

Shugaban kwamitin shari’ah na majalisar, Abubakar Sadik Jallo, wanda ya gabatar da kudirin a gaban majalisar a jiya, shine ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala zaman majalisar.

Abubakar Jallo ya kara da cewa an tsara wannan kudirin ne bisa tanadin dokokin addinin Musulunci na kare yara.

Kudirin dokar da aka tsara da nufin inganta rayuwar yara a jiharnan, ya kuma nemi a kara yawan kulawa da bayar da kariya ga yaran.

Bayan tattaunawa kan rahoton kwamitin, ‘yan majalisar sun amince da kudurin dokar da a yanzu ke jiran sahalewar gwamnan jiha kafin ya zama doka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: