Majalisar Wakilai Ta Nemi Gwamnati Ta Dauki Sabbin Malamai Don Magance Karancin Ma’aikata a Jami’o’i
Kwamitin kula da jami’o’i na Majalisar Wakilai ta Tarayya ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta amince da daukar malamai da sauran ma’aikata cikin gaggawa domin magance matsanancin karancin malamai da ma’aikata a manyan makarantu a fadin ƙasar.
Shugaban kwamitin, Hon. Abubakar Hassan Fulata, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce ana dora wa malamai da ma’aikata nauyin aiki mai yawa, wanda hakan ke rage ingancin karatun jami’o’i a Najeriya.
Fulata ya danganta karancin malamai da ma’aikata a jami’o’i da karancin albashi da rashin alawus-alawus masu inganci, yana mai kira ga gwamnati da ta hanzarta sake fasalin albashin jami’o’i, domin karfafa kwarin gwiwar malamai su ci gaba da aiki maimakon barin fagen, ko ficewar kasashen ketare.
Ɗan majalisar wanda ke wakiltar mazabar Kirikasamma, Guri da Birniwa a Majalisar Wakilai ya gargadi ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su daina tsoma baki cikin harkokin gudanarwar jami’o’i, saboda hakan na tauye ‘yancin hukumomin gudanarwar makarantu.
Hakazalika, ya roki Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) da ta janye niyyar shiga yajin aikin da aka sanar, yana mai cewa hakan zai kara dagula harkokin karatu da makomar ɗalibai a jami’o’i.