Kwankwaso Ya Goyi Bayan Mika Tikitin Shugaban Kasa Na 2027 Zuwa Kudu

0 69

Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana goyon bayansa ga matakin jam’iyyar NDC na mika tikitin takarar shugaban kasa na shekarar 2027 ga yankin Kudancin Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana cewa matakin ya dace da ka’idojin adalci, daidaito da kuma rabon mulki tsakanin yankunan ƙasar domin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a cikin jam’iyyar da Najeriya baki ɗaya.

Ya kuma jaddada muhimmancin bai wa kowane yanki damar jagoranci a tsarin dimokuraɗiyya domin tabbatar da haɗin kan al’umma da cigaban ƙasa.

Leave a Reply