Majalissar ƙaramar hukumar Guri tace ta gyara famfunan tuƙa-tuƙa 415 daga cikin 600 da ta tarar basa aiki a fadin yankin

0 153

Majalissar karamar Hukumare Guri tace ta gyara famfunan tuka tuka 415 daga cikin 600 da ta tarar basa aiki a fadin yankin.

Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Musa Shuaibu Muhammad Guri ya bayyana hakan ta cikin wani shirin Radio Jigawa.

Yace baya ga haka karamar hukumar ta gyara gidajen ruwa guda takwas daga cikin guda tara da ta tarar basa aiki.

Yace daga hawansa karagar mulkin karamar hukumar zuwa yanzu sun tara harajin fiye da naira miliyan tara.

Yace a shekara mai zuwa karamar Hukumar Guri zata mayar da makarantar firamare da Guri yamma zuwa tsohuwar tashar mota Guri da gina sabuwar tashar mota ta zamani a kusa da plantation da gina sabuwar tashar mota a Kadira da gina masalatan Juma’a a garuruwan Gaduwa da Zugo da Margadu da gyaran asibitin Arin da gina sabon asibiti a garin Wareri da samar da naurorin bayar da ruwansha a garuruwan Kadira da Wareri da Musari da Adiyani da lafiya da gina karin shaguna da runfuna a kasuwar Gwari wadda za a sauyawa matsugunni zuwa wajen gari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: