Matan Unguwar Dala Za Su Yi Saukar Alƙur’ani Domin Neman Zaman Lafiya

0 29

Ana sa ran matan al’ummar unguwar Dala da ke ƙaramar hukumar Dala a Kano State za su gudanar da saukar Alƙur’ani guda tara tare da addu’o’i na musamman domin neman taimakon Allah kan matsalar faɗan daba da rashin tsaro da ke addabar yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da taron ne a yau Alhamis, inda ake sa ran matan unguwar za su taru a ƙofar gidan Alhaji Shazali Ali da misalin ƙarfe tara na safe.

A cewar matan, sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon yawaitar ayyukan ɓata gari, faɗan daba da kuma matsalolin rashin tarbiyya da suka ƙaru a yankin cikin kwanakin baya.

Sun bayyana cewa addu’a da komawa ga Allah na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.

Haka kuma, matan sun yi kira ga iyaye da sauran al’umma da su haɗa kai wajen yaƙi da miyagun ayyuka tare da kula da tarbiyyar matasa domin tabbatar da ingantacciyar rayuwa da ci gaban yankin.

Leave a Reply