EFCC Ta Kama Darakta Janar Na Hukumar Makamashi Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 500

0 49

Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC sun kama Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Najeriya, Mustapha Abdullahi, bisa zargin hannu a wasu laifukan almundahana da kuma badakalar kuɗaɗe da suka haura Naira biliyan 500.

Rahotanni sun ce an kama shi ne a wani bangare na binciken da hukumar ke gudanarwa kan yadda aka tafiyar da wasu kuɗaɗen gwamnati da ake zargin an karkatar da su ba bisa ƙa’ida ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumar EFCC ba ta fitar da cikakken bayani kan yadda ake zargin an gudanar da almundahanar ba, amma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Ana sa ran cewa bayan kammala bincike, hukumar za ta bayyana matakan da za ta ɗauka a gaba kan shari’ar.

Leave a Reply