Hakan ya faru ne saboda wasu manyan alkalai masu rike da mukaman gwamnati da wadanda suka yi ritaya sun shiga cikin jerin sunayen da hukumar kula da harkokin shari’a ta tarayya, ta fitar a ranar Alhamis din da ta gabata.
Wani babban mai shari’a ya shaida wa manema labarai cewa, shugaban kasa Bola Tinubu zai iya fuskantar arangama kai tsaye da wani bangare na manyan ‘yan majalisar dokokin kasa, yana mai cewa “a tarihin Najeriya ba a taba nada alkalan kotun koli da aka sanya siyasa a ciki ba. Wani mai shari’a kuma ya ce shari’ar shiyyar Arewa ta tsakiya inda aka sanya dan tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, a matsayin fifiko yayin da wani babban malamin shari’a wanda ya haura shekaru 15 a kotun daukaka kara, aka sanya shi a matsayin a jiya.