Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta kama wani mutum bisa laifin fashi da makami da garkuwa da mutane a Ringim

0 177

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 27 bisa laifin fashi da makami da garkuwa da mutane.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, jiya a Dutse.

Shiisu Lawan ya ce, tawagar ‘yan sandan da ke aiki a Ringim ne suka kama wanda ake zargin.

Ya bayyana cewa ana kyautata zaton wanda ake zargin dan wani gungun ‘yan fashine da suka yi garkuwa da wani mutum mai suna Alhaji Ibrahim Jinjiri mai shekaru 60 a kauyen Zangon Kanya da ke karamar hukumar Ringim a watan Satumbar bara.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ya tunatar da cewa gungun sun yi garkuwa da wanda abin ya shafa bayan sun yi masa fashin naira dubu 300.

A cewar Shiisu Lawan, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: