Egbetokun ya ce Rundunar su ta fahimci muhimmancin mutunta ayyukan addini da al’adu da kuma bukatar kara hakuri da juna da hadin kai a tsakanin al’umma daban-daban.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar sanarwar tace Kayode Adeolu Egbetokun ya mika sakon rundunar ‘yan sandan ga daukacin al’ummar Musulmin kasar nan na watan Ramadan.
Bababn sifetan ya bukaci daukacin al’ummar musulmi da su rungumi tausayi, karamci, da gafara da ke tattare a cikin watan Ramadan. Ya kuma yi kira da a tallafa wa juna, da samar da zaman lafiya, da karfafa dankon zumunci da hadin gwiwa a cikin wannan wata mai alfarma da ma bayansa.