Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wani bisa zargin kashe dan uwansa

0 103

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wani mutum mai suna Isyaku Babale bisa zargin kashe dan uwansa saboda wata takaddama da ta barke a tsakaninsu.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil ya fitar a yau Litinin, yace an kama wanda ake zargin ne bayan da likitocin asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi suka tabbatar da mutuwar dan uwansa.

Sanarwar ta kara da cewa jami’an ‘yan sanda da ke hedikwatar ‘yan sandan a jihar sun kama wani mai suna Isyaku Babale dan shekara 30 a Anguwar Dawaki da laifin kisan kai. Ya ce, binciken da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin da wanda aka kashen sun kasance suna fada da juna ne da muggan makamai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: