Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce ta samu gagarumin ci gaba wajen magance munanan laifuka a jihar, inda ta samu nasarar cafke wasu mutane hudu da ake zargi da yin garkuwa da mutane da kuma wasu masu kera bindigogi a cikin gida.
Kakakin rundunar DSP Shiisu Lawan Adam shine ya bayyana haka a wata sanarwa.
Ya bayyana cewa an kama mutanen ne biyo bayan wani samame na hadin gwiwa da ‘yan sanda, da kungiyar ‘yan banga da kuma tattara bayanan sirri da jami’an tsaron suka yi.
Ya ce a ranar 16 ga Nuwamba, 2023, ‘yan sanda tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan banga na yankin, sun kama wani mai suna Bashir Muhammed mai shekaru 50 a kauyen Yan Dutsen Kawari, karamar hukumar Ringim.
A cewar DSP Shiisu yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin kerawa da kuma sayar da wadannan bindigogi ga wadanda ba a tantance su ba. Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka dake Dutse domin ci gaba da bincike.